1 Corinthians 6

Kaiwa Juna Kotu

1In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yǎ kai ƙara a gaban tsarkaka? 2Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shariʼa ba? In kuwa za ku yi wa duniya shariʼa, ai, kun isa ku yi shariʼa a kan ƙananan damuwoyi ke nan. 3Ba ku san cewa za mu yi wa malaʼiku shariʼa ba? Balle alʼamuran da suka shafi duniyan nan! 4Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan alʼamura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya! 5Na faɗi haka ne don ku kunyaya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba? 6Me zai sa ɗanʼuwa yǎ kai ƙarar ɗanʼuwa-a gaban marasa bi?

7Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku? 8Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ʼyanʼuwanku ne kuke yi wannan.

9Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku: Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ʼyan daudu, 10ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

Fasikanci

12“Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome”— sai dai ba abin da zai mallake ni. 13“An yi abinci domin ciki ne, cikin kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki. 14Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma. 15Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam! 16Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.”
Far 2.24
17Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.

18Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. 19Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

Copyright information for HauSRK